Hikayoyin kaifafa zukata

DAGA LITTAFIN MALAM AMINU KANO

Wasiyyar Annabi lukuman da dansa.

LBR:NA 004

Rubutu; Adam Muktar

Annabi lukmanu yayi zamaninsa na annabci a kan wa,a zi ga al umma wajen amru da nahyu.kuma irin abubban da yayi wa azi a Kansu har yanzu basu gushe su na da amfani ba.Abin tsoro da mamaki ma shine yanzu he ma aka fi bukatarsu. Galiban abubban daya farfafa suna nan dalla dalla a kur ani mai tsarki.Wasiyyar da ya yi wa dansa iri biyu ce .Ta farko ta kan wa azi gaba gadi.Ta biyu kuwa da misalai dan mai hankali ya lura.Zamu fi son yara su karanta irin ta misalin domin bata bukatar ilimi da zurfin hankali kafin a gane. An sanar cewa shi dan Annabi lukuman saurarayi ne mai ladabi da biyayya da kawaici.Ba abinda yake tsoro irin batawa mutane har saboda haka yake dari dari dasu .mahaifinsa ya yi ta kokarin nuna masa cewa in yasa aikin alheri a gabansa kada ya damu da abinda mutane zasu fada .Amma INA! Wata rana sai ya ce, da dansa ya jawo al fadarinsa suje yawo.Da rana tsaka ne kuwa.Annabi lukumanu ya hau , dansa yana korawa .Ga kuwa rana fatsi fatsir ,can sai wasu mutane suka ce ,don Allah kaga wani tsoho marar tausayi,ya bar yaro a kasa shi kuwa yana sama ya huta da zafi.Sai lukumanu ya sauka yasa dansa ya hau.Ba su he ko nan da can ba sai wani mutum ya ce ,kai wane irin yaro ne marar tausayi ,baka barin tsoho ya hau.?.Daga nan sai yaro ya sauka suka cigaba da kora alfadari.Da suka zo wani wurin sai wadansu dattijai suka ce,Yau ga wasu wawaye ,yaya cikin wannan rana mai zafi za Ku kora dabbar hawa maimakon Ku hau?.Sai lukumanu ya hau tare da dansa .Jimawa kenan da hawansu sai ga jama,a na cewa,wannan daukan alhaki da yawa yake.Yaya za a wahalar da dabba haka ? .Don me daya bai hau ba ,ko kuma su kora ta haka?:Daga nan lukumanu da dansa suka dawo gida ya ce da shi ,To,ya kai dana , kaga duniya yadda take . komai ka yi akwai mai kushe maka.Don haka in zaka yi Abu, ka auna ,in na alheri ne kayi gabanka gadi ,in ka daka ta surutun mutane sai ka mutu a zaune .; Dan Adam mai wuyar gane hali.

Comments