Posts

Showing posts from January, 2022

Hikayoyin kaifafa zukata

Image
DAGA LITTAFIN MALAM AMINU KANO NAN FA AKE YINTA LBR:NA08 Rubutu; Adam Muktar Da dadewa wadansu abokai uku suna zaune da daddare suna hira sai suka hangi wuta tana ci akan wani katon dutse.Dayansu ya ce," wannan dutsen da girma ya ke .ka ga wutan nan tafi kwana ashirin tana ci.: Sai dayan ya ce," Ai ta dunga yi kenan har fiye da kwana arba,in . Lallai dutsen nan na buli da girma yake,", Na ukun ya ce , A ina kuka ga girman dutse ba ku ga na kamaru ba . Ai in wuta irin wannan ta kama har shekara take yi tana ci.Sai suka ce, To malam da damina fa ? Malam sai ya ga ankama shi , bsshi da mafuta . sai ya ce, wane mutum ! . # Nan fa ake yinta." Sai suka bushe da dariya. Wato dai an gane mutuniyar a ka shara.

Hikayoyin kaifafa zukata

Image
Kome Dabararka Wani Ya Fika. LBR: NA 007 Rubutu; Adam Muktar Wata rana zakara ya yi sammako zuwa gidan suna a wani dan kauye . Ya yi nisa kenan sai yanyawa ta hange shi . saita sha kansa ta dawo kan hanya ta kwanta kashangare. Niyyarta da ya zo ta kama shi ta cinye. Zakara ya iso kusa da ita nan sai wani tsohon bera ya fito daga sunkuru ya ce da zakara ," Ina zuwa ? . Zakara ya ce , na ganta . Amma ai mushe ce ." Bera ya ce , ai da ranta; Domin yanyawa in ta mutu bakinta budewa yake yi. Da jin haka sai yanyawa ya bude bakinsa , sai bera ya ce , ka ga mushen naka ."Nan take zakara ya arce zuwa zuwa gida , yana mai godiya ga bera. Sai ya ce komai dabararka sai kaga wanda ya fika . maganin haka kawai a yi gaskiya.

Hikayoyin kaifafa zukata

Image
KASHI NA BIYU; YIN ISHARA GA MUTANE. ZURFIN HIKIMAR HAUSA. LBR'NA 006 Rubutu; Adam Muktar. Nan bada dadewa ba a kasar malumfashi an ace marakin wani bafillace.Rahoto ya kai ga yan doka , aka shiga bincike.Wani mai farin kaya mai bincike ya sami labarin kauyen da aka sayar da san amma bai sami sunan wanda aka ce ya saya har ya yanka ya sayar ba. An dai yi masa kwatance. Da ya zo kauyen sai ya zazzagaya a hankali har ya zo wani kofar gida inda ya tarar da wani dan yaro da magariba yana haka a jikin bango.Gidan kuwa a nan aka yanka sataccen marakin.Sai ya tambayi yaron ko a nan ne aka yanka maraki ?. Yaro ya ce ,'I, anan ne. Ashe uban yaron ya saurara. Sai ya ce ,kai waske ," kai da wa ? .Sai yaro ya gane cewa ya yi kuskure da ya amsa don haka ya waske .Sai ya ce, wani mutum ne da abin haushi.Ya same ni ina haka a ramin gafiya ko zan sami naman yau,sa,anan yake tambaya wai a nan aka yanka maraki?. Ni kuma don haushi na ce masa a nan ne .' don haka mai farin kaya ...

Hikayoyin kaifafa zukata

Image
DAGA LITTAFIN MALAM AMINU KANO LBR:NA 005 ++++++++++ ALHERI DAYA LADA GOMA Rubutu; Adam Muktar Koyaushe mutum ya yi wa wani ko wata alheri ubagiji zai saka masa da kamarsa ribi goma . sai dai in can cikin zuciyarsa akwai wata munakisa. wani dan taliki da matarsa da ya'ya biyu ya wayi gari ba shi da abinda zai ci kuma bashi da ko kwabo . Duk inda ya saba bubbugawa ya je bai samo ko da karfanfani ba. can la,asar sakaliya sai ya dawo gida hannu rabbana. Sai ya ce, da matarsa ta sa ruwa a tukunya ta dafa don ma yara su ga alamar ana abinci. Almuru ta kawo kai ke nan sai ya ji ana sallama a kofar gidanss. Da ya fito sai ga wani ya zo gare shi da cewa ya taimake shi da abinda zai ci domin tun safe bai sa hatsi a baki ba. Sai ya koma cikin gidansa ya ce da matarsa,"Yau ana wata sai ga wata," Kinji abinda mai sallaman nan ya kawo shi ? matarsa ta ce ," To yaya zaka yi ,banda ka sallame shi.? Ya ce," To ai abin da tausayi . Ba wani abu daza mu yi masa .? Ta ce ,...

Hikayoyin kaifafa zukata

Image
DAGA LITTAFIN MALAM AMINU KANO Wasiyyar Annabi lukuman da dansa. LBR:NA 004 Rubutu; Adam Muktar Annabi lukmanu yayi zamaninsa na annabci a kan wa,a zi ga al umma wajen amru da nahyu.kuma irin abubban da yayi wa azi a Kansu har yanzu basu gushe su na da amfani ba.Abin tsoro da mamaki ma shine yanzu he ma aka fi bukatarsu. Galiban abubban daya farfafa suna nan dalla dalla a kur ani mai tsarki.Wasiyyar da ya yi wa dansa iri biyu ce .Ta farko ta kan wa azi gaba gadi.Ta biyu kuwa da misalai dan mai hankali ya lura.Zamu fi son yara su karanta irin ta misalin domin bata bukatar ilimi da zurfin hankali kafin a gane. An sanar cewa shi dan Annabi lukuman saurarayi ne mai ladabi da biyayya da kawaici.Ba abinda yake tsoro irin batawa mutane har saboda haka yake dari dari dasu .mahaifinsa ya yi ta kokarin nuna masa cewa in yasa aikin alheri a gabansa kada ya damu da abinda mutane zasu fada .Amma INA! Wata rana sai ya ce, da dansa ya jawo al fadarinsa suje yawo.Da rana tsaka ne kuwa.Annabi lukuma...

Hikayoyin kaifafa zukata

Image
DAGA LITTAFIN MALAM AMINU KANO Labarin Annabi Muhammadu Da Bayahude LBR 003 Rubutu; Adam Muktar Wata rana annabi muhammadu(Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) Ya tara mutane yana wa, azi a madina sai wani bayahude yace yana da tambaya.Annabi ya ce; Allah ya sanarshe mu;Bayahude ya ce ;Ka ce komai a duniya nan yana cikin Al kur, ani.In haka ne ina ayar da ta nuna yawan gurasar da mudun al kama daya zai yi? Annabi ya ce; Akwai. Sai yasa aka kirawo wata mace mai yin gurasa ya tambaye ta.mai gurasa ta ce ;Ya manzon Allah idan an surfe zata yi gurasa uku, in kuma ba a surfe ba, ba za ta yi uku da rabi; Manzon Allah ya ce da bayahude , ; To ka ji; Bayahude ya ce ; Ai ayar nake so a kur, ani ba maganar mai gurasa ba; Annabi ya ce ; Allah ya ce; Ka tambayi ahlin abu , in baka sani ba, wannan mace ita ce ahlin gurasa ; A nan take Bayahude ya ce; Ka gaskata ya muhammad. Tammat bihamdillah

Hikayoyin kaifafa zukata

Image
DAGA LITTAFIN MALAM AMINU KANO Shugabancin Musulmi *********************** LBR: Na 002 Ainishin tsantsar shugabanci a tsakanin shugabannin musulmi aka samu.Kuma har yanzu ana samu nan da can .Farkon wadanda za a yi koyi dasu su ne halifofin farko da wasu da suka biyo bayansu.Haka kuma a nan kasar an sami manyan misalai da suka ishe mu koyi. Kuma shugabanci ba wucewa gaba ne kawai ba. Abu mafi wuya ma a cikinsa shine shugaba ya gane cewa sanya shi a gaba din ne biyansa ba ya tara wani abu ba,don tara dukiya ya shugabanci mutane haramun ne.Shugaba kullum yakan tsaya ya tabbatar hakkin mutane na gida da baki,dabbobi da tsirrai. Yazo cikin hadisi cewa sayyadi umar yardar Allah ta tabbata a gare shi kullum ba ya cin abincin dare sai anyi shela a madina ko wanda bai ci abinci ba.An tambaye shi dalili.Ya ce ,don kada Allah ya tambaye shi a ranar hisabi cewa yaya an bashi kiwon mutane amma ya bar daya da yuwwa,shi ko ya kwana a koshe ? Haka kuma yakan ce"wallahi in rakumi ya m...