Hikayoyin kaifafa zukata

DAGA LITTAFIN MALAM AMINU KANO

Labarin Annabi Muhammadu Da Bayahude

LBR 003

Rubutu; Adam Muktar

Wata rana annabi muhammadu(Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) Ya tara mutane yana wa, azi a madina sai wani bayahude yace yana da tambaya.Annabi ya ce; Allah ya sanarshe mu;Bayahude ya ce ;Ka ce komai a duniya nan yana cikin Al kur, ani.In haka ne ina ayar da ta nuna yawan gurasar da mudun al kama daya zai yi? Annabi ya ce; Akwai. Sai yasa aka kirawo wata mace mai yin gurasa ya tambaye ta.mai gurasa ta ce ;Ya manzon Allah idan an surfe zata yi gurasa uku, in kuma ba a surfe ba, ba za ta yi uku da rabi; Manzon Allah ya ce da bayahude , ; To ka ji; Bayahude ya ce ; Ai ayar nake so a kur, ani ba maganar mai gurasa ba; Annabi ya ce ; Allah ya ce; Ka tambayi ahlin abu , in baka sani ba, wannan mace ita ce ahlin gurasa ; A nan take Bayahude ya ce; Ka gaskata ya muhammad.

Tammat bihamdillah

Comments

Popular posts from this blog

MALIKUSSAIFI LITTAFI NA DAYA 05

MALIKUSSAIFI IBN ZIYYAZANUN LITTAFI NA DAYA-06

MALIKUSSAIFI LITTAFI NA DAYA 04