MALIKUSSAIFI LITTAFI NA DAYA 04

MALIKUSSAIF IBN ZAYYAZANUN -04

A lokacin da Wahshilfala ya kai shekara bakwai, sai ya buƙaci yana son ya fara hawa doki. Sarki ya sa aka ɗauko masa wani ɗan ƙaramin doki. Da Wahshilfala yaga wannan dokin sai ya rainashi ya ce, “Shi bazai hau wannan ƙaramin dokin ba, shi babba ya ke so. Sarki yasa aka mayar da wannan dokin aka kawo masa wani baƙin ingarman doki mai digo-digon fari a wuyansa da kirjinsa. Wahshilfala yace wannan doki yayi masa, yayi tsalle ya ɗare kansa ya yi sukuwa a gaban jama'a yana dawowa gaban sarki yana tirjiya. Daga nan Wahshilfala ya fara koyon yaƙi da takobi kuma cikin ƙanƙanin lokaci ya kware a harkar faɗa da takobi ya zamana kaf yaran dake sa'anninsa bawanda zai iya ja da shi har manyan ma. Ganin haka yasa Sarki Afarahu ya dinga alfahari da shi, kuma ya ware masa masu yimasa hidima. Wata rana sarki yana zaune a fadarsa da 'yan Majalisar sa ana fadanci can sai ga bokan Babban Sarki mai suna Saƙaradiyyuna ya shigo faɗar sarki da yan majalisa suka miƙe domin girmamawa ga wannan boka saboda sanin matsayinsa a gurin Babban Sarki wato Saif'ar'adu wato shugaban Sarki Afarahu. Boka Saƙaradiyyuna ya zauna, bayan sun gaisa da sarki ne sai boka Saƙaradiyyuna ya ce, masa yazo ƙasarsa ne ziyara, daga haka aka ci gaba da fadanci daga can sai Boka Saƙaradiyyuna yaga Wahshilfala zaune kusa da Sarki. Sai Bokan nan ya tambayi Sarki cikin rada mai ya kawo wannan farin yaron nan, kuma mai yake yi a cikin ƙasarka? shin ba ka da labari cewa irinsu ne zasu mulki duniya kuma su mai damu bayinsu bayan sun karkashemu. Nan take Sarki Afarahu ya faɗa wa bokan nan maganganu masu sanyaya zuciyar, Boka Saƙaradiyyuna ya yarda, da suka nitsa ne cikin hira sai Sarki Afarahu yake bawa boka labarin cewa ai matarshi ta haihu shekaru biyar da suka wuce, ta haifa masa 'ya mace. Nan da nan boka ya bukaci da akawo masa yarinyar ya ganta, Sarki ya sa aka kawo masa Shamatu domin boka ya samata albarka. Da boka ya daga ido ya kalleta sai yaga ai fara ce balarabiya, kuma ga shi tayi kama da wannan yaro Wahashilfala wanda Sarki yace ba dansa ba ne. Nan da nan boka ya yi tsafinsa ya gani cewa lallai wannan yarinya Shamatu yar Sarki Afarahu ce, kuma wannan yaro ba dansa bane. Sai ya umarci da ya mayar da wannan yaran cikin gida. Sarki ya tura Shamatu da Wahashilfala suka koma cikin gida. Nan dai Boka ya sake buka rairayi sai ya ga ita wannan yarinya wanda zai aureta farin mutum ne, kuma shine wanda zai mulki duniya, sai ya zaci ko Wahashilfala ne, sai ya fusata yace wa Sarki ya zama dole ya kashe wannan yaron Wahashilfala inkuma yaki to zai aika wa Dan uwansa Boka Saƙaradisa, ya faɗawa Sarki Saifu ce wa "Sarki Afarahu ya ajiye wani farin yaro kuma idan ya taso to duk zai halakar damu ne, sannan kuma ya mayar da wasun mu bayi. Boka Saƙaradiyyuna ya ƙare da cewa kaga kuwa idan Sarki Saifu ya ji wannan batu to labudda zai halaka ka da ki da jama'ar taka baki daya." Koda Sarki Afarahu yaji wannan magana daga bakin Boka Saƙaradiyyu na, kuma ya tuna matsayinsa a gun babban sarki, sai ya ce daboka najiwannan magana taka kuma na aminta amman bazan iya kashe wannan yaron ba, abin da zan yi shine zan rabashi da wannan ƙasa ta mu. Boka ya ji wannan magana sai ya aminta da maganar sarki Afarahu. Nan dai sarki Afarahu ya tura washilfala wani gari da ake kira Jiyada, ya aike mawani sadauki shi, wannan sadauki ana kiransa Aɗanɗamu, ya ce a koya masa dabarun yaƙi, shi wannan sadauki a wannan lokaci duk faɗin yankin Habasha babu sadauki kamarsa, kai har ta kai ta kawo duk sarakunan dake faɗin wannan nahiyar suna tsorosa.. Amma Boka Saƙaradiyyuna duk da cewar an dauke Washilfala amman hankalinsa bai kwanta ba, sai y fita cikin dare ya kama hanyar zuwa habasha, domin ya je ya kai wa sark Saifu'ar'adu labarin wannan yaro da yarinya, yana cikin tafiya da yake yana da ɗaurin ƙasa, tafiyar wata guda yana iya yinta a sa'a ɗaya, cikin wannan darehar ya kusa Habasha, sai ya haɗu da wani ɗan uwansa, wato ɗaya bokan mai suna Daƙiru. Saƙadiyyuna ya kwashe labarin Washilfala da Shamatu ya faɗa wa boka Daƙiru, koda boka Daƙiru yaji haka sai ya bugi ƙasa nan take wani baki aljani ya bayyana, boka Daƙiru ya umarci wannan aljani da ya tafi ƙasar Duwar ya ɗauke Shamatu yar sarki Afarahu, Aljani ya amsaya tafi. Shi wannan aljani ana kiransa Muftaɗihu, dama al'adarsa kenan kwashe mata ƴaƴan sarakuna ya kaisu can bisa wani tsauni inda ya yi gida. Bayan tafiyar wannan aljani sai boka Daƙiru ya ce ai wannan yarinya itace musabbabin da yaron zai dawo, to kaga yanzu idan wannan aljani ya ɗauke ta ya yi tafiyarsa da ita shikenan mun huta, gaba ɗaya suka kece da dariyar ƙeta. Boka Saƙaradiyyuna ya ce ni yanzu bari na koma ƙasar Duwar domin naga yadda zata kasance. Suka rabu, boka Daƙiru ya koma Habasha shi kuma boka Saƙaradiyyuna ya koma Duwar. Koda boka Saƙaradiyyuna ya koma Duwar sai ya iske wannan baƙin aljanin Muftaɗihu yana tsaye a ƙofar shiga birnin, koda zuwan boka cikin fushi sai ya ce me ka ke jira ne ka tsaya anan, maza kaje ka ɗauketa. Aljanin na ya faɗa wa boka cewar ai shi wannan birnin yana da wani kafi wanda ya hanani shiga a halin yanzu har sai nan da wata uku masu zuwa. Boka ya yi baƙin ciki da wannan abu, amman haka ya sallami Muftaɗihu, sannan ya umarci wannan aljani da cewar da zarar wata ukun ya cika ya zo ya ɗauke Shamatu sannan ya koma cikin birnin Duwar sannan aljani ya tafi. Can kuma a birnin Jiyada Washilfala yana ta koyon yaƙi wajen sadauki Aɗanɗamu, nan da nan ya ƙare wajen sanin dabarun yaƙi da iya sarrafa takobi kowanne iri sannan da iya wasa da doki. Aɗanɗamu tun lokacin da ya fara koyawa Washilfala yaƙi yake mamakin juriyarsa gami da ƙarfin da yaron yake da shi. A wannan lokacin Washilfala yana da shekaru bakwai a duniya amman idan ka ganshi sai kace ɗan shekara goma sha biyar ne, saboda jikinsa da manyan gaɓoɓinsa. A wajen da Aɗanɗamu ya ke gwajin makamansa akwai wasu bishiyoyi guda uku manya da yake jifansu da mashi yana hudawa, a cikin bishiyoyin nan akwai wata guda ɗaya wadda duk tafi sauran girma, sadauki Aɗanɗamu idan ya jefa mashinsa baya iya huda ta, sai wata rana yana koya wa yaron jifa, sai yaron ya daga mashinsa ya fuskanci wannan bishiya, koda Aɗanɗamu yaga haka sai ya bushe da dariya ya ce Bazaka iya da wannan bishiya ba domin ko nima nayi iya yina na kasa huda ta. Koda rufe bakinsa sai Washilfala ya fusata ya daga mashin da ke hannunsa sannan ya jefeta da shi, mashi kuwa ya fita daga hannunsa tamkar fitar kwari ya keta iska yana wata ƙara kai kace kububuwa ce, ya isa jikin bishiyar nan ya huda ta ya fice sannan ya yi tafiya mai nisa sannan ya faɗi ƙasa. Koda Aɗanɗamu yaga haka sai ya riƙe baki yana mamaki, yana rayawa a zuciyarsa cewar lallai wannan yaro idan ya girma a wannan ƙasa, darajar nan da ake bani saboda sadaukantakata to zai karɓeta, wata ƙilama ya kashe ni. Sai Aɗanɗamu ya kama Washilfala ya fita da shi can daji ya ajiye shi, sannan shikuma ya dawo gida. Washilfala ya yita tafiya baisan inda zashi ba, yana cikin tafiya sai yazo kusa da wani kogo ya ji ana nishi a cikin sa, da yaje wajen wannan kogon sai yaga wani tsoho, ashe shine ya ke wannan nishi. Da Tsohon nan ya ganshi sai ya ce Barka da zuwa Washilfala, koda Washilfala ya ji haka sai ya cika da mamaki ya tambaye shi yadda akayi yasanshi, sai tsohon nan ya faɗa masa cewar shiba mutum bane aljani ne, kuma yau shekaru ɗari uku da tamanin kenan a cikin wannan kogon yana gadin wata bulala. Da Washilfala ya ji wannan magana ta tsoho sai ya tambaye shi, me ye Amfanin wannan bulala? Da har ka kai waɗannan shekaru kana gadinta. . . Zan dakata anan sai Allah ya kaimu wani lokacin, idan Allah sake sadamu da ku. .

Comments

Popular posts from this blog

MALIKUSSAIFI LITTAFI NA DAYA 05

MALIKUSSAIFI IBN ZIYYAZANUN LITTAFI NA DAYA-06