MALIKUSSAIFI LITTAFI NA DAYA 05
Malikussafi ibn Ziyyazanu na daya - 05
Tsohon ya amsa da cewa ita wannan bulala idan aka daki aljani da ita konewa yake a take ya mutu, saboda haka duk wanda ya mallaketa to zai mallaki Aljanun duniya. Washilfala ya ce da tsohon to ina bulalar take, tsoho ya shiga da Malukussaif cikin kogon ya nuna masa bulala, koda yaga bulalar sai ya ce da da tsohon to ɗaukota mu gani, tsoho ya ce a'a ai bani da iko zuwa kusa da ita sai dai kai. Washilfala ya miƙa hannun ya ɗauko wannan bulala, koda tsohon nan yaga haka sai ya yi niyyar ya yi masa wayo ya ce, Bani na gani Sai Washilfala ya ce A'a bazan baka ba sai ka fitar da ni, kuma ka sani a hanyar zuwa garin Duwar. Da tsoho ya ji haka sai ya ɗaukoshi ya kawoshi kusa da garin Duwar ya ajiye shi, ya kuma nuna masa hanyar da zai bi ya shiga garin. Koda wannan tsohon ya sauke Washilfala sai ya raya a zuciyarsa ya ce Tunda wannan tsohon yace shi aljani ne bari na gwada akansa na gani in da gaske ne, sai ya daddage ya tsula wa wannan aljani bulala, nan take kuwa sai wannan aljanin ya kama da wuta ya ƙone kurmus. Koda Washilfala ya ga haka sai ya kama murna, ya daura wannan bulala a kubakar wandonsa sannan ya kama hanyar shiga birnin Duwar wato ƙasar sarki Afarahu inda ya girma. A wannan lokaci kuma baƙin aljanin nan da boka Saƙaradiyyuna su ka saka ya ɗauke Shamatu wa'adin daya ɗiba ya cika, har yazo garin ya ce A fito masa da Shamatu yar Sarki Afarahu domin gobe zai tafi da ita, in kuma ba hakaba to zai kifar da garin, sarki Afarahu da matarsa Dahashanatu suka yi ta kukan bakin ciki rabuwa da yarsu, amman shiko boka Saƙaradiyyuna sai farin ciki ya ke. Ya yinda gari ya waye, nan sai sarki Afarahu ya ce, Shi ba zai bayar da ƴarsa ba, da jama'ar gari suka ji haka sai suka ce akan ƴarsa guda ɗaya bazai sa a halakar da su gaba ɗaya ba, idan ba zai bayar da Shamatu ga wannan aljani ba to su duk zasu fice su bar masa ƙasar sa su barsa da ƴarsa da matarsa. Ganin haka yasa sarki ya sa aka fito da Shamatu, aka sanyata a cikin wata bukka, jama'a duk aka koma gefe ana jiran wannan aljani yazo ya ɗauketa. Ana cikin wannan hali na fargaba da jimami sai aka ga wani yaro ya shigo wannan gari, sai duk jama'ar suka haƙikance cewar wannan aljani ne yazo a suffar yaro, har sai da ya zo kusa sannan suka gane shi ashe Washilfala ne. Da zuwansa kamar ya sani sai ya zarce inda wannan bukka da aka sa Shamatu, ya iske ta tana ta kuka. Yana ganinta sai ya tambaye ta abinda yake faruwa, nan ta sanar da shi abin da yake faruwa. Sai Washilfala ya rarrasheta ya ce Tayi shiru zai kuɓutar da ita, ana cikin haka sai akaji rugugin wannan aljani ya keto ruwa ya shigo wannan gari, ya miƙa hannunsa ya cire rufin dake kan bukkar nan ya jefar, sai yaga Shamatu da Washilfala zaune a cikin wannan bukkar, ya miƙo hannu zai ɗauketa sai Washilfala ya zaro wannan bulala tasa ya tsula masa a hannu, nan da nan hannun aljani ya gutsire ya kama da wuta. Aljanin yayi wata irin ƙara ya juya da gudu ya faɗa ruwa. Yayin da wannan abu ya faru sai sarki Afarahu da matarsa Dahashanatu gami da sauran jama'arsa suka yita murna gami da kuɓutar da Shamatu da Washilfala ya yi daga sharrin wannan baƙin aljanin, kuma suna murnar dawowar Washilfala, aka yita shagali kwana da kwanaki, amman a ɓangaren boka Saƙaradiyyuna kuwa baƙin ciki ya tuƙe shi na kuɓutar Shamatu gami da dawowar Washilfala, amman sai ya boye ɓacin ransa ya nuna shima kamar murnar yake. Bayan shekaru goma da faruwar wannan abu, Washilfala ya cika shekaru goma sha bakwai da haihuwa ita kuma Shamatu tana ƴar shekaru goma sha biyar. Wata rana Shamatu tana tattaki acikin gidan sarautar sai tayiwo ɓangaren Washilfala tana ɗagawa, can sai ta jiyo wata murya mai daɗi ana raira waƙa, nan da nan sai ta matsa kusa da wata taga inda sautin wannan murya ya ke fitowa, sai ta gane ai wannan waƙa ta bege ce, kuma ita ake yi mawa, koda ta ƙare ma wanda ke waƙar kallo sai ta gane ai Washilfala ne yake raira waƙar, Sai tayi ajiyar zuciya tace, Daman Washilfala shima yana begena kamar yadda nake begensa tuntuni, sai ta yi Murmushi ta samu waje ta zauna t cigaba da sauraronsa har zuwa wani lokaci, can sai taji ya yi shiru data leƙa sai ta iske ya yi bacci, sai juya ta koma dakinta ta kwanta tayi bacci, amman ina domin zuciyarta ta ɗimauta da son Washilfala, hakata kwanta bata yi bacci ba, haka Shamatu ta kasance har tsawon tsahon mako biyu. Wata rana Shamatu ta je tana sauraron Washilfala yana waƙa, sai ta riƙa tunani to ai yakamata ta je ta sanar da shi ya je ya sanar da mahaifinta cewar yana neman aurenta. Da gama yanke wannan hukunci sai ta doshi ƙofar ɗakinsa ta kwankwasa masa ƙofa. Sai Washilfala ya ce, wa ye? Ta amsa da cewar Washilfala ne Da Washilfala ya ji haka sai ya yi mata izni da ta shigo, bayan ta shigo ta iskeshi yana zaune sai ita ma ta zauna. Ya tambayeta lafiya ya ganta cikin wannan daren? Ta amsa da cewar amman banyi zaton cewa zaka yi mani irin wannan tambayarba, domin yadda nake ji kullum kana begena. Da Washilfala ya ji haka sai yasan Lallai taji baicikan da yake raira mata, ya dube ta ya ce, Ashe ke duk kinsan halin da nake ciki na sauƙin begenki da nake yi. Ta amsa masa da cewa Eh, kuma daman itama ta daɗe tana son sa, amman ta kasa bayyana masa saboda kunya, haka dai suka yi ta hira irin ta masoya har dare ya raba, sannan Shamatu ta tashi ta nufi ɗakinta, ya yin da shima Washilfala ya kwanta bacci. Haka dai Washilfala da Shamatu suka ci gaba da soyayyarsu har ta yi ƙarfi, har mutane suka fara sanin abin da ake ciki. Wata rana Shamatu tazo wajen Washilfala suna fira, sai Shamatu ta zauna kusa da Washilfala, sai ya miƙe tsaye ya matsa daga kusa da ita ya ɓata ransa. Sai ta tambaye shi ta ce ya abin begena me yasa kake guduna ko baka sona ne? Da Washilfala ya ji wannan magana daga Shamatu sai ya ce mata ai ni bana nufin yin wasa da ke, inba aurarki nayi ba, domin ni a ganina wannan bai dace ba. Da taji wannan bayani nasa sai ta yi Murmushi ta ce Gaskiya ne, to amman mai zai hana gobe idan ka fita faɗa ka nemi aurena a wajen ubana. Da Washilfala ya ji ta bashi wannan dama sai ya ce ba damuwa gobe zai aikata hakan, tunda dai kin yarda zaki aure ni, suka ci gaba da hira har dare ya raba Shamatu ta koma cikin gida Washilfala kuma ya kwanta bacci kamar yadda suke yi a kullum. Gari na wayewa Washilfala ya shirya ya fito fada ya zauna kusa da sarki, ana ta fadanci, yana so ya faɗi maganar da suka yi shida Shamatu jiya amman kuma saboda ganin yawan jama'ar da ke fada sai kunya ta kamashi, har aka tashi daga fada bai faɗa ba. Da dare Shamatu ta je wajensa, bayan sun gaisa ta tambayeshi shin ka aikata abin da na umarceka jiya kuwa? Washilfala ya gaya mata ai bai faɗa ba domin ya taradda da fada a cike, kunya ta hanashi faɗa. Da jin haka sai tace Kash! Kai yanzu kunyar jama'a sai ta sa ka tauye rayuwarka ta hana ka cimma burinka, ta ce ai kawai gobe idan ka je ka faɗa, tayi ta ƙarfafa masa gwuiwa ta ce masa ai kawai gobe ya faɗa kada ya ji kunyar jama'a, ya faɗi abin da ke ransa, Washilfala ya sake amsa mata zai faɗa, bayan sun gama firar ne kamar yadda suka saba, Shamatu ta koma cikin gida. Da gari ya waye Washilfala ya fito fada kamar jiya amman sai yaga ina ya kasa faɗa wa sarki wannan magana. Bayan ya shigo gida da daddare sai Shamatu ta je wajensa kamar yadda ta saba, da suka gaisa sai ta tambayeshi To ya ya yau ka faɗa? Ya amsa mata ai yauma ya kasa faɗa, koda Shamatu ta ji haka sai ranta ya ɓaci har ta fara hawaye shi kuma ganin haka sai ya ce ai gobe ya zama lallai y faɗa kada ta damu, haka dai suka yi ta yi har lokacin rabiwarsu ya yi ta tashi ta fita. Kashe gari Washilfala ya shirya ya fito fada sai yaga a wannan rana fada bata taɓa cika irin wannan rana ba, da yaga haka da shigarsa sai ya haɗe fuska ya ɓata rai, yaje wajen da ya saba zama amman bai zauna ba har zuwa wani lokaci, can sai sarki ya fuskanci lallai akwai wani abu da ke damun Washilfala sai ya tambayeshi Ya ɗana ya yau na ganka ba kamar yadda na saba ganinka ba, me ya faru gareka Washilfala ya amsa wa sarki da cewa ni ba wani abu bane ya dameni, illa kawai so nake ka aura mani Shamatu. Da jin wannan magana sai hankalin boka Saƙaradiyyuna ya tashi, ranshi ya ɓaci, fuskarsa ta yi duhu. . . Zan dakata anan sai Allah ya kaimu wani lokacin, idan Allah sake sadamu da ku.
Comments
Post a Comment