MALIKUSSAIFI IBN ZIYYAZANUN LITTAFI NA DAYA-06
Fassarar Aliyu Abubakar Sharfadi . Ya dubi Sarki Afarahu ya ce Shikenan ga abin da muke gudu nan ka jawo mana. Koda sarki Afarahu ya ji abin da boka ya ce akan maganar da Washilfala ya faɗa sai ya ji tsoron kada bokan nan ya je ya shirya masa wani makircin a wajen babban sarki, sai ya yi dabara ya ce da Washilfala ai wannan ba wani abinda zaka damu kanka ba ne, domin kuwa kaine kafi cancanta da ka aureta, kodan kuɓutar da ita da kayi daga hannun wannan baƙin aljanin Muftaɗihu, na riƙeka ɗane a wajena, ita kuma Shamatu na wakilta boka Saƙaradiyyuna ya zamo waliyinta, saboda haka yanzu a wajensa zamu nemi auren. Koda boka Saƙaradiyyuna ya ji an damƙa ragamar aure a hannunsa sai ya yi murmushi yana rayawa a zuciyarsa ya samu hanya mai sauki ta halaka Washilfala. Sarki Afarahu ya dubi boka Saƙaradiyyuna ya ce Yaro yana neman auren yarinya mene ne dukiyar aurenta? Boka ya yi dariya ya ce Kasan neman auren ƴaƴan sarakuna ƙasaitattu irinka yana da tsada sosai, to mu yanzu ba dinare, azurfa ...