MALIKUSSAIFI LITTAFI NA DAYA 03

Malikussafi ibn Ziyyazanu na daya - 03

Shi wannan mutumin, mutumin ƙasar Duwar ne, kuma ita wannan masarauta ta kasance ta na ƙarƙashin Ƙasar Habasha ne. Da Isar wannan Maharbi gida tun daga waje ya Fara kwala wa matarshi Kira harya shiga cikin gidan. Da isar shi ya miƙa mata yaron, kana ya sakko da akwatun da yake a kansa, sannan ya kwashe labari kaf! Ya bata. Ya ce, "Kinga shikenan daman bamu taɓa haihuwa ba ga shi Allah ya bamu ɗa, sannan kuma ga dukiya Allah ya bamu." Da matar ta ji haka sai ta ce "Haba! Mai gida kai ka dubi irin wannan kyakkyawan yaron, da ganinsa kasan dan sarakuna ne, ko kuma manyan attajirai ta ya ya zamu iya rikeshi? Kuma kaga shi farine muko duk baƙaƙe ne, ai ana gani za a ce sato shi muka yi aje a samu a cikin wani hali, kawai yanzu ka daukeshi kaje ka kai wa Sarki shi domin wannan yaro yafi karfin mu." Da mijin ya ji haka sai ya zauna ya yi tunani, kuma sai ya aminta da shawarar matar ta shi. Saboda haka sai ya kinkimi akwatun sannan ya ɗauki jaririn ya nufi gidan Sarki. Yana isa bayan ya yi gaisuwa ga Sarki, ya kwashe labari Kaf ya labarta wa Sarki. Sarki ya karɓi wannan jaririn daga hannun maharbin nan. Shidai wannan Sarki sunan sa Afarahu, kuma ya kasance ƙaramin Sarki ne dake ƙarƙashin babban Sarki wato sarki Saifu na Habasha. Sarki Afarahu daman bai taɓa haihuwa ba, sai ya yi murna da samun wannan jaririn, ya baiwa matarsa mai suna Dahashanatu ya ce "Ta riƙeshi duk da su baƙaƙe ne, shi kuma wannan yaron fari ne {Balarabe). . ***************************** . Ita kuma can wannan Aljanar da ta ba jaririn nan nono ya sha, da ta koma gida, sai take bawa mijinta labarin cewa "Ta ga wani jaririn mutum kwance a daji shi kadai, ta daukeshi ta bashi nononta yasha." Da mijin yaji wannan labari sai ya ce "Ai tunda kika ba shi nononki ai ya zama danki saboda haka yi maza kikoma ki daukoshi." Nan da nan Aljana ta bazama nema. Ta koma kasar Duwar. Ta duba inda ta bar jaririn nan amman sam bata ganshi ba, sbd haka saita je wurin Sarki Aljanu na wannan garin domin shima a ƙarƙashin mulkin mijinta ya ke. Ta nemi da ya baza dakarun Aljanu su nemo mata wannan jariri duk inda yake. Nan da nan Aljanu suka bazama cikin ƙasar domin gano inda jaririn nan ya shige. Jim kaɗan sukazo da labarin cewa ai yaron yana gidan Sarki Afarahu. Nan da nan aljanar nan ta juye ta koma izuwa siffar mutane, ta iske matar Sarki tana rungume da jariri, tana shiga sai ta ce “Nazo ne na karɓi ɗana. Koda Dahashanatu taji wannan batu sai ta fusata, jin cewa wata tazo zata rabata da wannan yaro. Na da nan sai tayi kiran wasu bayi ta faɗa masu suyita dukan Aljanar nan Harsu fitar da ita. Da Aljana taji haka sai tayi wani ruri wanda ya firgita duk wanda ya ke gidan, ta kuma faɗa masu ita ba mutum bace, saboda haka su bata jaririn nan ko kuma ta halakasu gaba dayansu. Dahashanatu taji tsoro, sai ta kama kukan bakin cikin rabuwa da zata yi da shi. Nan ta tura aka kira sarki ta bashi labarin abinda yake faruwa, nan take shima Sarki ranshi ya ɓaci ya umarci matarsa da ta miƙa wa wannan aljanar yaron. Dahashanatu ta miƙa mata yaron cikin bakin ciki. Koda aljana ta ga irin hallin da suka shiga sai tausayinsu y kamata, tace masu yanzu zan tafi da shi na ci gaba da shayar da shi, amman idan ya cika shekara biyu zan dawo maku dashi. Da gama ɗaukar wannan alkawari, sai wannan aljanar tayi sama da yaron bata zame ko ina sai a fadar mijinta, wato Sarkin fararen Aljanu. . ***************************** . Can kuma a Hamra'u Yemen, Sarauniya Ƙamriyya sai ta faɗa wa jama'arta cewr ai wannan yaro ya mutu. Koda jama'a suka ji haka mafiyawancinsu basu yarda ba, amman saboda zafin mulkinta sai suka yi shiru domin sun san lallai idan suka ƙaryata zancenta, to lallai zasu ɗanɗana kuransu. Kuma ga shi duk mutanenta ne a majalisar, wann dalilin ne yasa suka bita a yanda tace. . ***************************** . Shi kuwa jinjirin da aljana ta ɗauka yayin daya cika shekara biyu a fadar Sarki Afayaru, sai aljana ta yayeshi tare da yarta, kuma ta nemi izini a gurin mijinta kan cewa tanabson maidashi gun Sarki Afarahu. Da Sarki Afayaru ya ji haka sai ya ce da ita tabar yaron nan a wajensu, ya ci-gaba da cewa yaron yana da alamura masu girma, domin kuwa dan Sarki ne, kuma shi zai kubutar da 'yarki daga wata masifa a nan gaba, kuma wannan yaro shine zai yaƙi duniya baki daya kuma yabyi nasara, saboda wannan girman lamari nasa nake ganin bai kamata mu kaishi wajen mutane yan uwansa ba domin zasu iya cutar da shi. Koda Dasuƙatu matar Sarkin aljanu taji haka sai tayi na'am da wannan magana, amman kuma sai ta tuna ai ta ɗaukarwa Sarki Afarahu da matarsa alkawari kan cewa zata maido da shi. Anan sai tace da mijinta eh ta yarda da maganarsa amman itama tana da shawara. Ya tambayeta yace to faɗi shawararki mu ji. Dasuƙatu tace kaga mu ba mutane bane, saboda haka halayyarmu da ta mutane ba iri ɗaya bace, zaifi kyau mu mayar da shi gurin mutane yan uwansa domin ya samu tarbiyya irin ta su. Sarki Afarahu ya yarda da wannan shawara ta matarsa, ya kuma yi mata izini da ta mayar da yaro gurin Sarki Afarahu da matarsa, amman ta ja masa kunne kada ya yarda wani abu ya taɓasa. Dasuƙatu ta ɗauki yaro ta mayar da shi ga Sarki Afara da matarsa kamar yadda tayi alkawari kuma ta gargaɗeshi kamar yadda mijinta ya faɗa mata. Sarki Afarahu ya karɓi yaro ya shiga da shi cikin gida cike da farin ciki, ya kira matarsa Dahashanatu ya miƙa mata yaron. Koda ta ganshi sai tayi wuf! ta karɓeshi, ta rungumeshi tana kuka domin farin ciki da murna da suka kamata. Sannan ya faɗa mata duk sharuddan da aljana ta faɗa masa. Anan Sarki da matarsa suka sama wannan yaro suna Wahshilfala. Bayan an samu kwananki Kamar kwana Arba'in da dawo da Wahshilfala wurin Sarki Afarahu, sai matar Sarki ta sami ciki, murna kan murna wurin Sarki Afarahu da matarsa Dahashanatu ba sai an faɗa ba, ga shi suna murna aljana ta dawo masu da Wahshilfala ga kuma Dahshanatu tana da ciki. Duk gari aka yi ta taya Sarki murna. Haka dai lokaci yayi ta tafiya har lokcin haihuwar Dahshanatu ya yi, ta haifo 'ya mace aka saka wa yarinyar suna Shamatu. Wannan yarinyar farace kuma sai ya zamto Kamarsu ɗaya da Wahshilfala. Wannan lamari ya baiwa Sarki Afarahu tare da duk sauran mutane mamaki, saboda su dai ga su baƙaƙe amman ga shi sun haifi farar mace, balarabiya, kuma ga shi tayi kama da wannan yaro Wahashilfala, haka dai suka yi ta manaki. . . Zan dakata anan sai Allah ya kaimu wani lokacin, idan Allah sake sadamu da ku

Comments

Popular posts from this blog

MALIKUSSAIFI LITTAFI NA DAYA 05

MALIKUSSAIFI IBN ZIYYAZANUN LITTAFI NA DAYA-06

MALIKUSSAIFI LITTAFI NA DAYA 04