MALIKUSSAIFI IBN ZIYYAZANUN LITTAFI NA DAYA-06

Fassarar Aliyu Abubakar Sharfadi

. Ya dubi Sarki Afarahu ya ce Shikenan ga abin da muke gudu nan ka jawo mana. Koda sarki Afarahu ya ji abin da boka ya ce akan maganar da Washilfala ya faɗa sai ya ji tsoron kada bokan nan ya je ya shirya masa wani makircin a wajen babban sarki, sai ya yi dabara ya ce da Washilfala ai wannan ba wani abinda zaka damu kanka ba ne, domin kuwa kaine kafi cancanta da ka aureta, kodan kuɓutar da ita da kayi daga hannun wannan baƙin aljanin Muftaɗihu, na riƙeka ɗane a wajena, ita kuma Shamatu na wakilta boka Saƙaradiyyuna ya zamo waliyinta, saboda haka yanzu a wajensa zamu nemi auren. Koda boka Saƙaradiyyuna ya ji an damƙa ragamar aure a hannunsa sai ya yi murmushi yana rayawa a zuciyarsa ya samu hanya mai sauki ta halaka Washilfala. Sarki Afarahu ya dubi boka Saƙaradiyyuna ya ce Yaro yana neman auren yarinya mene ne dukiyar aurenta? Boka ya yi dariya ya ce Kasan neman auren ƴaƴan sarakuna ƙasaitattu irinka yana da tsada sosai, to mu yanzu ba dinare, azurfa ko jauhari muke da ɓukata ba, abu na farko da muke da ɓukata wajen neman auren Shamatu shine ya je ya zo mana da kan ɗan fashin nan mai suna Sa'adunzanji shine abu na farko da muke da ɓukata. Ko da sarki ya ji wannan buƙata sai ya girgiza kai domin yasan Washilfala bazai iya faɗa da wannan ɗan fashin ba balle har yazo da kansa, sai sarki ya ce ayi masa sassauci domin wannan ya yi tsauri da yawa. Washilfala ya yi farat ya ce Babu komai zan kawo kan wannan ɗan fashin. Jin haka sai sarki ya yi shiru domin ba yadda zai yi tunda Washilfala ya amsa, aka tashi daga fadanci. Da dare ya yi Shamatu ta zo wajen Washilfala kamar yadda ta saba, bayan sun gaisa sai ta ce da shi Ya zaka amsa wa kanka abin da kasan cewar ba zaka iya ba, na samu labarin cewar ance ka ce Wai zaka iya yaƙi da wannan ɗan fashin, kasan wannan mutumin kuwa? Ya ce, A'a sai kin gaya min. Shamatu ta fara da cewa na samu labarin cewar shekarun baya da suka wuce, shidai wannan ɗan fashin mai suna Sa'adunzanji yana zauna ne a wani daji yamma da birnin Siriya, a kwana a tashi har ya yi wani birni a cikin wannan dajin inda suke zaune shi da yaransa su Tamanin, kuma banda shi da yaran nan nasa babu wani wanda yasan abinda ake faɗa ƙofar birnin nan ta buɗe. Shi wannan ɗan fashin yana tare ayarin fatake ya yi masu fashin dukiyoyinsu kuma ya korasu birnin sa su zama bayi, kai har takai ta kawo yana shiga birane yana yiwa sarakuna fashi saboda ƙarfinsa dana jama'arsa su Tamanin, wanda daga cikin mutanensa idan ya tura yara huɗu suna iya yaƙar gari guda su yashe dukiyoyinsu kuma su kamo jama'ar garin. Kai saboda girman jiki na waɗannan mutane basa hawa doki sai giwa, a takaice dai hatta babban Sarki Wato sarkin Habasha ya yaƙi ɗan fashin nan amman bai samu nasara ba, dole haka ya haƙura ya ƙyaleshi sannan ka ce kai ɗaya zaka je ka yaƙesa, ai ni nasan bazaka iya ba. Koda Washilfala ya ji wannan labari na Shamatu maimakon zuciyarsa tai sanyi amman sai ta harxuƙa, ya tashi ya ɗauko kayan yaƙinsa ya fara sakawa, ya ce da Shamatu Ai ni yanzu tunda ma har kin faɗa mani a dajin da yake to ni yanzu ma zan tafi. Nan fa hankali Shamatu ya tashi domin tasan ba makawa idan Washilfala ya yi ido biyu da wani daga cikin yaran Sa'adunzanji to fa kwanansa ya ƙare, domin kuwa zasu shayar da shi gidauniyar mutuwa, nan dai Shamatu ta yi ta lallashin sa akan ka ya tafi amman ina zuciyar maza ta motsa, koda ta fuskanci baya da alamar fasawa sai ta roƙe shi akan ya yarda su tafi tare. Ya ce A'a shi sam bai yarda ba, daya gama shirinsa tsaf, ya hau dokin sa ya kama hanya cikin daren ya yi ta tafiya har ya fita daga cikin ƙasar Duwar ya nutsa cikin daji yana tafiya, can yana cikin tafiya ya fito cikin wani dan fili sai yaga wani sadauki ya yi shirin yaƙi ya suƙwano dokinsa a guje ga takobi zare a hannun sa, nan da nan shima Washilfala ya zare tasa takobin. Wannan sadaukin ya yiwo kan Washilfala tamkar zakin dake jin yunwa ya hango nama. Nan dai suka hau junansu da sare sare kowa yana kai wa kowa sara, haka dai suka yi ta yi har gari ya waye rana ta fito wani daren ya sake yi, suna cikin wannan dauki ba daɗin ne sai Washilfala ya fusata ya miƙa hannu ya fisgo wannan sadaukin daga bisa dokinsa, ya murɗeshi ya bugashi da ƙasa, ya zaro wata wuƙa daga ƙugunsa zai caka wa wannan sadaukin, koda sadaukin nan ya ji Washilfala ya yi masa riƙon tsauri kuma yana ƙoƙarin halakashi, sai ya yi wuf! Ya yaye rufin mayanin dake bisa fuskarsa, sai Washilfala yaga ashe Shamatu ce suke yaƙi da ita ba wani barde bane. Koda yaga haka sai yai sauri ya ɗagata sannan ya tasheta tsaye ya tambayeta Me yasa ki ka yi mani haka? Nayi maka haka ne domin na jaraba jarumtakar ka naga ko zaka iya yaƙar Sa'aduninzanji ko a'a, yanzu na tabbatar da cewa kai jarumi ne to amman inason ka yarda na bika mu tafi tare. Koda Washilfala ya ji cewa har yanzu Shamatu tana nan kan bakanta na son tafiya tare da shi, sai shi kuma ya sake nanata mata rashin yardar sa na cewa ai sam bazai yiwu ba, bazaki bini ba. Shamatu ta yi ta yi ta shawo kansa amman ya ƙi, wannan abu ya ɓata masa rai har tayi masa baki tace In Sha Allahu ni zan zamo sanadiyyar kuɓutarka daga wani haɗari da zaka shiga nan gaba a wannan tafiya. Bayan wannan magana ta ta, sai ta kada linzamin dokinta ta yi kamar ta koma gida. Shi kuma ya miƙa ya yi gaba yana 'yan waƙe-waƙensa irin na mayaƙa. Ita kuma Shamatu ko da ta ga ya yi nisa sai ta biyoshi a baya ba tare da ya sani ba. Bayan yan kwanaki sai Washilfala ya iso gindin dutsen nan na birnin Sa'aduninzanji, ya koma can gefe gindin wata ƙatuwar bishiya ya sauka daga bisa dokinsa ya zauna. A wannan lokaci itama Shamatu ta iso gindin wannan bishiya bai sani ba, sai itama ta samu guri ta ɓuya, can zuwa wani lokaci sai suka ji hayaniyar mutane sun nufo inda su ke suna ihu, ashe wasu mutane Sa'aduninzanji ne suka koro wasu mutane da yawa da dabbobi, koda isowarsu daidai inda Washilfala ya ke ɓoye sai ya yi wuf ya shige cikin mutanen nan da aka koro shima sai aka kora tare da shi ba tare da sanin waɗannan yan fashin ba. Haka itama Shamatu ta shiga cikin wannan ayari na kamammu ba tare da sanin kowa ba har Washilfala. Da suka ƙarasa daf da dutsen nan sai ɗaya daga cikin mutanen Sa'aduninzanji yai waɗansu maganganu kalma huɗu sai dutsen nan ya tsage suka shiga cikin birni, da shigarsu sai suka tsaida kamammun nan, su kuma mutanen Sa'aduninzanji suka hau wata matattakala suka haye sama. Jim kadan sai Washilfala ya nufi wannan matattakalar ya taka ta farko, ya kuma miƙa ƙafa izuwa ta biyu daga takawarsa sai ta rufta da shi, wasu wuƙaƙe masu tsananin kaifi gami da tsini suka taho zasu rabashi biyu. Nan da nan sai Shamatu ta rugo da gudu ta yi wuf ta jawoshi waje, Koda ya ganta sai ya tambayeta Shamatu ya akayi kika zo wajen nan. Ta kwashe labarin kaf ta faɗa masa koda ya ji sai ya ce To shikenan gashi nan addu'ar ki ta ci. Nan Shamatu ta fara ba shi labarin wannan matattakalar ta ce, Ai ita wannan matattakalar idan ka taka ta farko lafiya to ta biyun sharri ce, sai ka taka ta samanta sannan zaka wuce, haka kuwa suka yi har ya hau can sama, da suka hau sai suka ga wata ƙatuwar ƙofa ta baƙin ƙarfe, Washilfala ya leƙa sai ya hango wani baƙin mutum ƙato, mai manyan idanuwa jajaye kamar garwashin wuta, gashi da ƙaton hanci kamar gwangwani, sannan da katon kai gami da manya manyan labba kamar fatar dabba, yana zaune akan wani gado, a gefensa na dama akwai sadaukai arba'in haka gefensa na hagu. Da Washilfala yaga haka sai ya dawo ya laɓe daga gefen wannan ƙofa, ita kuma Shamatu tana daga bayansa. Sai ta ce da Washilfala shi wannan mutumin na tsakiya shine Sa'aduninzanji. Suna tsaye can sai Sa'aduninzanji ya ce da mutanensa Kai kutsaya ni fa motsi nake ji, inaga wani daga cikin mutanen da kuka kamo ya kwance, sai ya umarci ɗaya daga cikinsu ya fita ya dubo. Mutumin ya tashi da gaggawa ya nufo bakin ƙofa, yana fitowa sai Wahashilfala yayi wuf ya sare masa kai da takobin dake hannunsa, ita kuma Shamatu ta janyeshi ta ɓoye gawar. Da aka jima sai Sa'aduninzanji ya kuma turo wani barden, shima yana fitowa Wahashilfala ya kuma sare masa kai kamar yadda ya yi wa na farko. Haka Sa'aduninzanji ya yi ta turo mutane Wahashilfala yana kashesu har sau hudu, ana biyar sai ya ce da su wani ya tashi yaje amman sai aka rasa wanda zai je. Shi kuma Wahashilfala da yaga anjima babu wanda ya sake fitowa sai ya kutsa kai cikin wannan daƙin ya tsaya a gabansu. Koda suka ganshi sai Sa'aduninzanji ya bude baki cikin mamaki ya ce, To, kai kuma wannan ƙaramar halitta daga ina? Kuma mai ya kawoka nan harka halaka mani mutane? Babu abin da ya shafeka da sanin daga inda nazo, kuma dalilin zuwana nan shine nazo ne domin na kasheka na ɗauki kanka a matsayin sadakin aurena. Koda Sa'aduninzanji ya ji haka sai ya bushe da dariya ya ce kai yanzu wannan yaro ka iya yaƙi da ni? Dubeka fa ka dubeni na ninka ka sau goma, yanzu kaiko wannan saurauyin wane ne ya turoka ka aikata wannan abu gareni? . Washilfala cikin bacin rai ya ce ba'a sani ba idan zaka yi shirin yaki ka yi. Anan sai Sa'aduninzanji ya fusata ya ce zo mu shiga cikin gidana akwai fili isasshe wanda zai ishemu ni da kai har muga wanda zai yi nasara. Sa'aduninzanji ya tashi yaransa suka biyoshi a baya, Washilfala ma ya biyo shi a baya, suka shige wasu manyan soraye guda uku suka riski wani fili, da suka isa wannan fili sai Sa'aduninzanji ya juyo wajen mutanen sa ya ce idan muna yaki da wannan yaro kar wanda ya kawo mani dauki koda kuwa kunga yana kokarin samu galaba a kaina ne, ku tsaya kawai kuyi kallo. Koda yaran Sa'aduninzanji suka ji haka sai su dukansu suka babbake da wata mahaukaciyar dariya, domin sun san cewa ba ta yadda za' ayi wannan karamar halittar ya iya kai shugaban nasu kasa ko yazo da matemaka bare ya zo shi kadai. Suka amsa da sunji, sun yarda. Can kuma Shamatu da ta ga sun shiga wannan gida, sai ta fito daga inda take ɓoye ta hau kan wani dutse inda zata iya ganin karawar da za'ayi tsakanin Sa'aduninzanji da saurayinta. Nan dai aka ƙulla yarjejeniya yaƙi Sa'aduninzanji ya zare takobinsa ya yiwo kan Wahashilfala yana gurnani tamkar zakin dakejin yunwa ya hango nama, Wahashilfala shima ya zare tashi takobin ya yi ɗauki kan sa suka kaure da yaki bají-ba-gani har dare yayi rana ta take. Can suna cikin wannan ɗauki ba dadi dine sai Wahashilfala ya taka wani karamin dutse ya zame ya durkushe ƙasa. Sa'aduninzanji ya daga takobinsa ya kawo wa Wahashilfala wani wawan sara koda Shamatu ta ga haka sai ta tabbatar da cewa indai har saran nan ya dira a kan masoyinta to saidai wani bashi ba. Sai tayi wuf! Ta zaro wani gariyo daga cikin sulkenta ta wulwuloshi ta jefi Sa'aduninzanji da shi, sai gariyon ya sare shi a hannu wanda hakan yayi sanadin faduwar takobin dake hannunsa. Wahashilfala ya rike takobinsa a hannu yayi niyyar sarewa Sa'aduninzanji kai amman sai ya fasa ya ce, tashi ka ɗauki takobinka muci gaba da yaƙi, domin bazan kasheka ta hanyar yaudara ba, sai kuma ya juya ya fuskanci dutsen da Shamatu ta ke tsaye ya ce, jinjina gareki ya ma'abociyar bege. . Zan dakata anan sai Allah ya kaimu wani lokacin, idan Allah sake sadamu da ku. . . Domin samun wannan shahararren littafin akan lokaci sai ku ziyarci wannan Page ɗin nawa mai suna

{ DUNIYAR BAHAUSHE}

Comments

Popular posts from this blog

MALIKUSSAIFI LITTAFI NA DAYA 05

MALIKUSSAIFI LITTAFI NA DAYA 04