MALIKUSSAIFI LITTAFI NA DAYA
Fassarar Aliyu Abubakar Sharfadi
Godiya ta tabbata ga Allah madaukakin Sarki da manzonSa Annabinmu Muhammad, tsira da amincin Allah Su ƙara tabbata a gareshi, wanda ya bamu iko ga jama'a domin su samu abin ɗebe kewa da nishadantarwa yayin karantashi. Shi wannan littafin, fassarace daga harshen larabci zuwa na hausa domin jama'a Su amfaneshi. Shi wannan littafi mafi yawancin mutanen yanzu basu sanshi ba, domin Malamai ne ada suke karanta wa jama' a shi idan suna jin nishadi. Zaku ji cewa Wannan littafin ya kunshi labaran soyayyaya, nishadi da kuma abubuwa iri daban-daban, wadanda suka kunshi sha'anin bokanci da tsafe-tsafe wanda mutanen wancann lokaci suka kware a kai. Za kuma aji yadda rayuwa take kasancewa ga wannan sarki, tun tasowar sa da kuma girmansa, kama izuwa lokacin daya zama kasaitaccen Sarki da kuma mutuwar sa. Kuma za aji cewa wannan littafin ya shafi ɓangaren addini da kuma ma'amaloli na rayuwar al'umma. Malukussaif Ibn Ziyyazinun a karan kansa an taba samu rayuwa irin tasa. ldan muka duba tarihin masarautar Borno zamu samu cewa daya daga cikin wadanda suka taɓa yin sarauta a wannan masarauta wadanda akeyiwa laƙabi da Saifawa Dinas (Wato Daular Saifawa), tayi kimanin Shekara dubu kafin ta gushe, wannan zuria ta saifawa sun samo sunansu ne daga wannan babban Sarki kuma kamar yadda tarihi ya nuna shine ya kafata. Don haka labari da aka bayar akan wannan Sarki Saifu yana iya zama kirkirerren labari, ko kuma shi Sarkin ya zamto antaɓa samun sa. A hakikama yankin da wannan sarkin ya zauna wato Hamra'u yemen ko Yemen wato kamar yadda wannan littafin tarihin ya nuna. . A wani zamani mai tsawo da ya wuce, zamanin annabi Nuhu (AS), ya yiwa 'ya'yansa addu'ar Allah ya sa daya daga cikin su a xuriyarsa a samu wanda zai mulki duniya, kuma ya yada addinin Allah. Cikin ikon Allah sai addu'ar sa ta faɗa kan babban dansa Samu, wanda shi Samu a wannan lokacin zuriyarsa farare ne Larabawa. Shi kuma qaramin dansa Hamu xuriyarsa baqaqe ne. Bayan sun bar gurin mahaifinsu, sai shi Samu ya nufi gabashin duniya, shi kuma Hamu ya nufi yammacin duniya. ! Bayan wani lkc mai tsawo sai aka yi wani Sarki, mai suna Ziyyazanun, shi wannan Sarki ire-iren zuriyar Samu ne. A wannan lkc ya samu tarihin addu'ar da Annabi Nuhu (AS) yayi wa kakansu Samu, ta Allah ya sa a irin zuriyarsa a samu wanda zai mulki duniya, kuma ya yada addinin Ibrahimiyya, da yake a wannan zamani, zamanin Annabi Nuhu (AS) ne ! Sarki Ziyyazanun a wannan lkcn sai ya lashi tokobin in Allah ya yarda a kansa wannan addu'a zata fada, saboda haka ya yi ta yaƙe-yaƙe a ƙasashen duniya, har ya faɗo yammacinta yana ta yaƙi har tsufa ya fara kama shi. Wata rana Sarki Ziyyazanun da jama'arsa suka sauka a wani wuri, sai ya ga yanayin wannan waje yana da kyau kuma yana da dadin zama. Don haka sai ya gina birni, ya saka masa suna Hamra'u Yemen. Shi wannan birni da ya gina yana qarqashin masarautar Habasha ne. Wadda a lkcn kuma qasar Habasha tana qarqashin mulkin Sarki Saifu'ar'adu ne, wanda shi kuma ire-iren xuriyar Hamu ne, wato su baqaqe ne. Sarki Saifu'ar'adu ya sami labarin cewa ga wani Sarki can fari, ya sauka a qasarsa ya gina birni, ba tare da izininsa ba. Don haka sai ya tura 'yan leqen asiri domin su gano masa irin shirin Sarki Ziyyazanun, suka je suka dawo, suka gayawa Sarki Saifu'ar'adu cewa ai Sarki Ziyyazanun ya zo da rundununa ta sadaukai masu yawa. Kuma suka gaya masa cewa ai ma ba zai iya yaƙarsa ba. Nan da nan Sarki Saifu'ar'adu ya sa aka tara masa bokayen ƙasar Habasha, domin su ba musulmi bane. Taurari suke bautawa. Ya umarci bokayen nan da su duba su gani, idan ya yaqi Sarki Ziyyazanun akwai nasara ko babu? Bokayen nan suka duƙufa, suka kama bincike, kowanne ya yi, sai ya ga babu nasara. Ƙarshe dai, suka gayawa Sarki Saifu'ar'adu kada ya yaƙi wannan Sarki. Domin babu nasara. Sarki ya sallame su suka watse. Sarki Saifu'ar'adu ya sa aka kirawo masa wasu manyan bokayensa masu suna Saƙaradisa da Saƙaradiyyuna da Wazirinsa mai suna waziri Baharu. Nan da nan wadannan mutane guda uku suka zo gaban Sarki Saifu'ar'adu suka zauna, Sarki ya ce yana so ne su bashi shawarar yadda zai 6ullowa Sarki Ziyyazanun. Da bokayen nan suka ji wannan buqata ta Sarki. Sai suka ce. “Tauraruwa ta baka nasara. Ai abin da za ka yi kawai shi ne, ka ɗauki ɗaya daga cikin yardaddun kuyanginka. Ka bata guba, ka ce kana so ta 6oye ta a jikinta, inda kowa ba zai iya ganinta ba, idan ta 6oye sai ka tura ta ga Sarki Ziyyazanun a matsayin kyauta ta karramawa. Ita kuma, sai ka umarceta idan ta tashi baiwa Sarki abinci ko abin sha, ta saka masa gubar nan a ciki. Da ya ci ko ya sha, sai ya mutu. Ka ga shi kenan ba sai mun yaqe shi ba." Sarki Saifu ya yi murna da jin wannan shawara ta boka Saƙaradiyyuna. Nan da nan ya sa aka kira masa wata kyakkyawar kuyanga yarinya, daga cikin yardaddun kuyanginsa, mai suna ƙamriyya. Aka kawo guba ya bata ya ce ta 6oye ta a inda babu wanda zai ganta koda caje ta aka yi. Qamriyya ta kar6i gubar nan ta cusa ta a cikin gashin kanta, yadda in ba wanda ya sani ba, babu mai iya ganewa, sannan kuma Sarki ya gaya mata cewa zai bayar da ita ga Sarki Ziyyazanun, idan ya kar6eta suna tare, ta san yadda zata yi ta bashi wannan gubar ko a abinci ko a abin sha, ya ci ko ya shi. Ya ce idan ta aikata haka, to zai 'yanta ta, kuma zai bata dukiya mai yawa. Idan kuma ta kasa yin hakan, to muddin ta dawo Habasha to zai halakata. Qamriyya ta yarda da hakan. Sarki ya hada ta da 'yan aike, ya ce su tafi xuwa Hamra'u Yeme, su kaiwa Sarki Ziyyazanun ita. ! Shi kuwa Waziri Baharu, wanda yake musulmi ne, ya musulunta ne ba tare da sanin Sarki Saifu'ar'adu ba, domin kuwa da Sarkin ya san da musuluncinsa, da tuni ya sa an halaka shi, sbd gudun abin da zai same shi sai ya 6oye musuluncinsa bai bayyana ba. Kishin addini ya sa ya kasa jurewa kan makircin da aka qullawa Sarki Ziyyazanun, hankalinsa ya tashi, sbd ya san lallai Sarki Ziyyazanun ba zai iya gane makircin da aka shirya masa da Qamriyya ba. Domin haka sai ya rubuta takarda xuwa ga Sarki Ziyyazanun. Yai bayanin cewa shine wazirin Sarki Saifu, ya kuma ce masa shi musulmine ya kuma yi masa bayanin duk irin makircin da aka shirya game da ƙyautar Ƙamriyya da za a kawo masa, duk ya rubuta a wannan takarda. Daya gama yai kiran wani yardajjen bawansa ya bashi wannan takarda ya ce "Yai sauri ya riga yan aiken Sarki Saifu zuwa wannan sabon Birni na Hamra'u Yemen, ya kai wa Sarki ziyyazinun wannan takarda ba tare da wani mutumin Habasha ya ganshi ba. Sannan kuma ya faɗa masa cewa idan ya aikata hakan ya dawo to zai ƴantashi kuma zai bashi dukiya mai yawa. Waziri ya bashi takarda wannan ya suƙwani doki ya bi ta wata ɓarauniyar hanya ya nufi Hamra'u Yemen cikin dare ba tare da kowa ya ganshi ba. zan dakata a nan.
Comments
Post a Comment