MALIKUSSAIFI LITTAFI NA DAYA 02

Fassarar Aliyu Abubakar Shafadi

Waziri ya bashi takarda wannan ya suƙwani doki ya bi ta wata ɓarauniyar hanya ya nufi Hamra'u Yemen cikin dare ba tare da kowa ya ganshi ba. Bayan kwana uku sai aka yi Sa'a wannan bawa na waziri Baharu ya riga ƴan aiken sarki Saifu zuwa Hamra'u Yemen. Da zuwan sa cikin hanzari ya isa fada aka yi masa iso gurin Sarki, da shigarsa ya faɗi ya yi gaisuwa sannan ya miƙa wannan takarda ga Sarki Ziyyazinun, ya umarci Sarki da a sallameshi da wuri, domin kada ƴan aiken Sarki Saifu su iso su taradda shi suyi tsammanin wani abu ne. Nan Sarki ya yi masa ƙaututtuka sannan ya sallameshi, shi kuma ya kama hanyar sa ta komawa birnin Habasha. Bayan kamar sa'a uku da tafyar bawan nan sai ga ƴan aiken Sarki Saifu sun iso wannan birnin. Da zuwansu suma sai suka wuce fada aka yi masu iso suka shiga sannan suka yi gaisuwa gaban Sarki, kuma suka isar da saƙonsu Sarki Saifu na ƙyautar Ƙamriyya da Sarkisu Sarki Saifu ya ba wa Sarki Ziyyazinun. Koda Sarki Ziyyazinun yaga wannan saƙo sai ya sake gaskata bayanin da Waziri Baharu ya faɗa masa, amman dukda haka sai Sarki Ziyyazinun ya karɓi Ƙamriyya ya nuna kamar baisan makircin da ake shirin ƙulla masa ba. Ya sa aka bawa yan aikennan masauki, suka kwana kashe gari ya sallamesu suka kama hanya izuwa ƙasar Habasha. Bayan ansamu kamar wata ɗaya. Wata rana sai Sarki Ziyyazinun ya kaɗaita da kuyangar da aka kawo masa wato Ƙamriyya, a wannan Iokaci ya zare takobinsa ya umarceta da ta fito da gubar da aka bata ta bashi, in kuma taƙi to zai halakata, da Ƙamriyya ta ga zai halakata, sai ta ciro gubar daga kanta ya karba, sannan suka kwanta tare a wannan dare dai Sarki Ziyyazinun bai gushe ba saida kuyanga Ƙamriyya ta samu ciki dashi. Da Sarki ya ga ta samu ciki sai ya kira wani malaminsa ya ce, ya buga masa ƙasa ya gani. Sai wannan Malamin ya ga ai wannan ciki na Ƙamriyya namiji zata haifa, kuma shine wanda zai mulki duniya. Sai ya faɗa wa Sarki wannan labarin, Sarki yayi murna kwarai. Daga nan sai Sarki Ziyyazinun ya rinƙa nunawa Ƙamriyya kauna yana tattalinta. Lokacin da cikin Ƙamriyya ya cika wata na huɗu sai Sarki Ziyyazinun ya kwanta ciwon ajali, inda ya yi wasiyya cewa idan ya mutu Ƙamriyya ta hau karagar mulkinsa har ta haihu, idan Dan ya girma ta sauka ta ba shi mulkinsa. Bayan yan kwanaki ya cika inda Ƙamriyya ta ci gaba da mulki kasar Hamra'u Yemen. Da aka samu yan kwanaki Ƙamriyya tana kan gadon sarauta sai ta rika ɗauko mutanen Habasha ɗai-ɗai da ɗai-ɗai tana kawosu majalisar ƙasar Hamra'u Yemen, ta na kuma korar mutanen Sarki Ziyyazinun suna mutuwa. Cikin dan ƙanƙanin lokaci duk ta kori mutanen Sarki Ziyyazinun daga majalisar ta mayesu da sababbi. Ba dadewa sai cikin Ƙamriyya ya kai wata tara, ta haifi yaro namiji kyakykyawa fari, tamkar mahaifinsa. Tun lokacin da Ƙamriyya ta haihu, kuma taga ta haifi na miji sai wani abu ya dinga ɗarsuwa a zuciyarta. Bayan gari ya waye sai Ƙamriyya ta shirya jaririn ta fito da shi domin jama'a su ganshi, bayan ta zauna ne bisa karagarta sai ta ajiye jaririn daga gefe bisa wata shimfida wadda ba kowanne jariri ake kwantarwa akai ba sai 'ya'yan manyan Sarakuna. A wannan lokaci duk jama'ar da suka zo fada a wannan rana, sai suka rinƙa zuwa wajen wannan jariri suna kwasar gaisuwa suna cewa "Yaron kuwa kamarsu ɗaya sak da ubansa suna cewa munyi mubayi'a, su na cewa sarkinmu na gobe." Bayan sun gama kwasar gaisuwa gaban jaririn tare da masa addu'ar Allah Ya raya, sai kuma su juya kan Ƙamriyya suyi gaisuwa. Ganin cewa tun yanzu, tun ba'aje ko ina ba gashi an fara mancewa da ita, sai ta wannan jaririn ake yi sai kishi ya kamata, anan sai tasan gabama lallai tuɓe ta zasu yi su naɗa wannan yaron. Ƙamriyya ta boye abin da ke damunta a zuci, da dauki yaron ta koma cikin gida da shi, jama'a kowa ya watse. Da isarta gida sai Ƙamriyya ta zauna tayi shiru tana tunani, hankalinta ya yi ƙololuwar tashi domin tasan lallai idan wannan yaron ya taso, ya girma ya samu wasiyyar uban sa to lallai sai ya tureta daga gadon sarauta ya hau, kuma gashi ita ta ɗanɗana giyar mulki taji da daɗi. Saboda haka ta yanke shawarar kawai ta kashe shi shiya fi. Ta ɗauko wuƙa zata yankashi amman sai ta fasa, ta sake yunkurawa zata yanka shi sai ta fasa, ana uku da ta kuma yunƙura zata yan kashi, sai wata tsohuwar kuyanga ta shigo dakin, koda ganin abin da ke shirin faruwa sai tace “Kai! kai! Ke ko me wannan jariri ya yi ma ki da har kike yunkurin hallakashi? Nan Ƙamriyya ta faɗa wa wannan tsohuwar dalilinta, da tsohuwa taji haka sai ta bata shawarar kada ta yankashi, ta bari sai dare ya tsala su hau dawakai su biyu, su sulale ba tare da kowa ya gansu ba suje can daji su yarda shi, kana su ajiye dukiya tare dashi domin duk wanda ya tsincesa yayi amfani da wannan dukiya wajen rainonsa, domin idan ya taso hannun wani, bazai taɓa tunanin shi ɗan Sarki bane balle ma har yayi wani tashin hankali. Sarauniya Ƙamriya ta yarda da wannan shawara ta tsohuwa, ta fasa yanka shi, ta bari har dare ya raba sannan su ka sulale kamar yadda tsohuwa ta faɗa, suka yi ta tafiya, har saida suka fita daga cikin ƙasar, kana su ka ajiye jaririn a gindin wata bishiya, kuma su ka ajiye akwati cike da kuɗi, sannan suka yi komawarsu. Can cikin dare, jariri ya farka ya fara kuka shi kadai a cikin daji, can yana ta kuka sai matar Sarkin fararen aljanu tazo giftawa tana ɗauke da 'yarta mai suna Akisa, wadda a wannan lokacin tana shayar da ita. Da aljanan nan ta ga jinjirin nan sai tausayinsa ya kamata, sai ta tsaya ta daukesa ta ba shi nononta yasha ya ƙoshi, daya ƙoshi sai ya koma bacci, ita kuma ta ajiyeshi ta ɗauki 'yarta tayi gaba. Can da asuba tayi jaririn nan ya sake farkawa, ya kama kuka yana cikin kukanne sai ga wata barewa mai shayarwa tazo wajen, ta ga jaririn nan sai ta tsugunna ta kara masa nononta yasha. Yana cikin Sha ne kawai sai wani maharbi ya hango barewar nan. Aiko ya lallaɓo ya na sanɗa saboda barewar bata ganshi ba, koda ya matso kusa sai yaga ai barewar nan jariri Ɗan mutum ta ke baiwa nono, sai ya tsaya ya na mamaki har dai barewar nan ta ganshi ta gudu. Maharbin nan ya matso kusa da yaron nan ya tabbatar ɗan mutum ne, kuma ga wata akwatu kusa da shi, daya buɗe akwatun yaga dukiya sai ya maida ya rufe, ya dora akwatin a bisa Kai, ya kuma dauki jaririn ya rungumeshi, ya na murna ga dukiya ga kuma Yaro sun samu. Saboda haka ya Juya akalarsa zuwa gida. Zan dakata Anan sai Allah ya kaimu wani loka

Comments

Popular posts from this blog

MALIKUSSAIFI LITTAFI NA DAYA 05

MALIKUSSAIFI IBN ZIYYAZANUN LITTAFI NA DAYA-06

MALIKUSSAIFI LITTAFI NA DAYA 04