Gabatarwa

HIKAYOYIN KAIFAFA ZUKATA

NA MALAM AMINU KANO

Assalamu alaikum warahhamatullahi ta,ala wabarakatuhu.Bayan haka kamar yadda muka sani a kowane zamani a ko'ina a duniya za a ga koyaushe mutane suna da hanyoyin koyar da ya'yansu hankali tsinkaya da basira jurewa hakuri azanci da dabara da dai sauran halayen da za su taimake su lokacin da za su fara ma'amalantar mutanen zamani. Daya daga cikin hanyoyin nan yakan kasance iya amfani da harshe wajen magana.Daga nan sai labarai na gaske dana almara,zaurance,karin magana,azancin tatsuniya,habaici,wa,azi,waka,cita cita da sauransu. Harshen hausa ko kadan bai gaza ba wajen wadan nan ba.haka nan kuma wajen labaran ban dariya,azanci,tausayi,wayo da dabara. Ganin abbubban nan sun fara bacewa a kasar nan,da kuma ganin rashinsu zai tauye mana wata daraja nan gaba balle ga bada ilimi kyauta ga ya'yanmu yazo, na dauki nauyin rubuta wannan dan littafi da fatan taimakawa a wannan siffa.kuma ina kara fata da addu,a cewa zai zama kafin alkalami ne ga sauran marubuta. Mai karatu zai ga na debo abubban daga sassa :harda labarai na gaskiya bayan na almara saboda manufa dai ita ce kaifafa zukatan yara don kafin su girma su sami wukar gindi maganin aron ta wani.Allah ya yi mana muwafaka. Daga karshe ina so in mika godiyata ga yan kwamatin inganta hausa na cibiyar nazarin harsunan nigeriya jami,ar bayero ,kano musammamma marafan sakkwato alhaji ahmadu da dr.dan datti abdlkadir dr.kabiru galadanci,da alhaji abdlmalik mani da alhaji usman mai riga,da alhaji abdullahi khalil da m.ibrahim yaro yahaya wanda suka karfafa mini gwiwa a taron da mukayi a sakkwato cikin watan octoba 1976 kan wallafar wannan littafi don tarbiyar yaran mu da inganta hikimomin hausa.

Kano:21 janairu,1977. Tammat bihamdillah Rubutu:

Adam Muktar

Comments

Popular posts from this blog

MALIKUSSAIFI LITTAFI NA DAYA 05

MALIKUSSAIFI IBN ZIYYAZANUN LITTAFI NA DAYA-06

MALIKUSSAIFI LITTAFI NA DAYA 04