Hikayoyin kaifafa zukata
IMANI SHINE TABBATAR AIKI
Rubutu;
Adam Muktar
An yi wani malami da almajirinsa . Banda karatu dayake dauka a wajen malamin har yakan tambaye shi nakulkula.A cikin irin haka ne har yabawa almajirin wata addu,a wadda in an karanta ta ana iya taka ruwa a wuce. Ana cikin haka sai tafiya ta kama malamin zuwa wani dan kauye. A daren tafiyar anyi ruwa kwazari har korama ta kawa. Da suka iso koramar sa almajiri yace "Yau ga ranar addu,a " sai ya karanta ya taka ruwa caf-caf-caf ya haye.Malami ya karanta ya taka sai tsulum ya tsunduma . Ya nanata amma a banza sai yaro ya takayo ya dawo .Malami ya karanta dai dai da yaro amma ya tsulluma , yaro kuwa ya haye .Malami ya gigice ya ga ya ya haka. Can sai yaro yace" malam naga s duk inda kuskuren yake.Na ga kai in ka karanta sai ka ja wondonka sama .Ni kuma ai ko wannan tunanin ba bana yi balle in ja wandona. Tunda aka ce a taka a wuce , yaya kuma za,a yi tunanin jikewa
Comments
Post a Comment