Gobe Jar Kasa 01
Gobe jar kasa
LITTAFIN SHAFI'U DAUDA GIWA
. TANA a zaune akan katifarta ita kadai a cikin dan karamin dakinta ta dade a haka tun kusan kimanin awa daya tana kallon kundin adana hotunanta (album) wanda ta rikeshi da hannuwanta biyu kamar littafin karatu Duk da yake ta rufe kofar dakin nata hakan bai hanata ganin hotunan ba ta hanyar hasken kwan wutar dake goshin dakin wutar babu karfi wani lokacin ayi kamar za'a dauketa zuwa can kuma sai ta tsaya batayi mamakin haka ba don kuwa ruwa aketa shekawa a daidai lokacin kamar da bakin kwarya ga kuma iska da walkiya don haka za'a iya dauke wutar akowane lokaci bayan yanzu Duk lokacin da akace ana ruwa indai wannan budurwar tana gida sau da yawa babu abinda tafi sha'awa irin ta dauko hotunanta na da Dana yanzu ta rika kallonsu tana tunanin abubuwan da suka gabata a rayuwarta A haka zata wuni a cikin dakin nata har zuwa lokacin da za'a dauke ruwan Idan ta gaji saita fito waje tasha iska ko kuma taje dakin mahaifiyarta suyi hira Sabanin sauran ranakun da irin haka yasha faruwa da ita yau ruwan ya sauko ne a daidai lokacin da take shirin zuwa asibiti inda take aiki yanzu aikin rana take yi karfe sha biyu saura kwata take fita ta isa asibitin da karfe sha biyu dai-dai daga nan bazata dawo ba sai kuma karfe bakwai na yamma * Gashi yau ruwan ya tsareta har taci kusan awa daya a gida tana jira a dauke don haka tanadai kallon hotunan ne a wannan karan don kada ta rasa abinda zatayi a dakin nata amma badon tana so ba Sannu a hankali taci gaba da bude shafukan hotunan tana cin karo da hotunanta Wadanda ta dauka ita da kawayenta tun a shekarun baya da suka shude tana da kokari wajen adana hotuna da wahala ta dauki hoto ta yarda ya salwanta Da haka take tunawa da yawancin kawayenta wadanda suka yi karatu tare tun a sakandire tun suna aji daya wadanda wadansu da yawa a cikinsu yanzu ita kanta bata san inda suke ba a duniya ko a raye ko a mace Allah kadai ya sani Yawancin hotunanta na da sunfi dadin gani don kuwa ta daukesu ne cike da farin ciki suna dafe da juna ita da kawayenta sunsa kayan makaranta iri daya sun dafa juna suna dariya kowacce sanye da hijabi gwanin ban sha'awa . A shekarun baya sa'ar da tana karama a zahiri tafi jin dadin rayuwa Saboda a waccan lokacin babu wani abu da yake damunta tana rayuwarta cikin kwanciyar hankali da farin ciki Amma yawancin hotunanta wadanda basu wuce shekaru uku ba ta daukesu ne a cikin damuwa wanda kai tsaye za'a iya gane hakan ta hanyar ramewar da tayi a cikin hotunan yanxu kam tafi zama mace sosai amma indai za'a dauko hotunan nata a hadasu waje daya da an gansu za'a fahimci rayuwa ta canza da ba yanzu ba . Duk da yake hotunan nata suna debe mata kewa a boye suna tayar mata da hankali wani lokacin ma har kuka suke sata a dakin nata ba tare da kowa ya sani ba shiyasa ba kowanne hoto take so ta rika yawan kallo ba a kowanne lokaci. . Hotunan da ta dauka ita da kawayenta sunfi komai debe mata kewa don kuwa da yawa a cikinsu sunyi aure wadansu ma yanzu sun haihu yakai uku ita kadaice har yanzu tana nan a gida harta fara aiki amma kama-kama auren bai kankama mata ba tukunna Ko yanzu da take zaune a dakinta tana jiran daukewar ruwan bata yadda tayi nisa a cikin (album) din ba shafi uku kawai ta bude na farko inda hotunanta na can baya suke a zamanin da tana 'yar sakandire Zuwa can kuma saita sake bude shafi na gaba acan ne taci karo da wani hotonta guda daya data wareshi shi kadai saboda tsabar son shi da take yi tunda take a duniya bata taba daukar hoton da ya fito da ita ba ya baiyana kyawawan siffofinta irin wannan hoton yawanci shi tafi ba duk wani saurayi da ya dameta ta bashi hotonta don kuwa tasa an wanke mata wannan hoto yafi kala talatin daga bara zuwa bana Duk ta raba su saura wannan guda daya da ya rage yanzu a cikin (album) din nata wanda tayi alkawarin ba wanda zata bashi Indai ba wani tasa aka wanke ba Sanye take da tsukakkiyar jar riga wacce ta kama jikinta tunda daga tsakiyar mararta har xuwa bisan kirjinta ta lankwasa dogon wuyanta a cikin hoton tayi tagumi da yatsanta daya sanan tana sanye da bakar hular sanyi wacce batayi nasarar suturce yalwataccen dogon gashin kanta ba da ya zubo har zuwa dogon wuyanta tana sanye da farin siket wanda ya dan leko kadan a cikin hoton ta hanyar durkusawa da tafi ta dafa gwiwarta da daya hannun tana kallon kyamara da kyawawan idanunta dake kama da kankara ba murmush take yi ba ta tsayar da hankalinta ne a waje guda duk da haka idan ba lura mutum yayi ba sai ya rantse murmushi take yi a cikin hoton Wannan ya samo asali ne saboda kyalkyalin da lebbanta sukeyi a dalilin wani rantsastsen man lebe da tayi ado dashi sa'ar da ta dauki hoton shekara daya da rabi kenan da ta wuce . CIGABA...... Loading
Comments
Post a Comment