Waken Suya
YADDA A KE NOMAN WAKEN SUYA
Wace kasa waken suya yake bukata? waken suya yana bukatar kasa wacce take Ita ba tabo ba bakuma yashi ba wannan kasar Ita waken suya yafi bukata amma Ana yi a yashi da tabon amma gaskiya bai fiya bada abunda ake so ba sannan sai a haro da huda. Yaushe ake shukar waken suya? Ana shuka waken suya ne bayan an tabbatar ruwa ya tsaya bawai anayin ruwan farko ko na biyu kaje kai shikaba sai ruwa ya tsaya sannan sai ka shuka saboda idan ba laima a tare dashi har ya kwanta to baya tashi sai dai ka sake shuka wani idan zakai shukar anasa 3 zuwa 4 a rami daya sannan bayan kwana 10 zakazo kai kwafi ma'a duk inda bata fitoba kasake shukawa. Sannan bayan sati 1 zuwa kwana 10 sai ai noma sannan sai ka barshi har sai lokacin da ya fara fure sai azo ai huda. Shin waken suya yana bukatar taki? Waken suya baya bukatar taki mutukar ka zuba takin gargajiya a farko kafin a karce wajan baka bukartar zuba wani taki saboda yana samarwa kansa taki da kasa. Yaushe ake girbe waken suya Ana girbe waken suya bayan ruwa ya dauke ya bushe sosai sai a girbeshi sannan a barshi ya kara bushewa tsowan kana 4 zuwa 7 sannan sai azo a bugeshi sannan a zuba a buhu a kaishi rumbu a ajjiye.
Comments
Post a Comment