Hikayoyin kaifafa zukata
Kome Dabararka Wani Ya Fika.
LBR: NA 007
Rubutu; Adam Muktar
Wata rana zakara ya yi sammako zuwa gidan suna a wani dan kauye . Ya yi nisa kenan sai yanyawa ta hange shi . saita sha kansa ta dawo kan hanya ta kwanta kashangare. Niyyarta da ya zo ta kama shi ta cinye. Zakara ya iso kusa da ita nan sai wani tsohon bera ya fito daga sunkuru ya ce da zakara ," Ina zuwa ? . Zakara ya ce , na ganta . Amma ai mushe ce ." Bera ya ce , ai da ranta; Domin yanyawa in ta mutu bakinta budewa yake yi. Da jin haka sai yanyawa ya bude bakinsa , sai bera ya ce , ka ga mushen naka ."Nan take zakara ya arce zuwa zuwa gida , yana mai godiya ga bera. Sai ya ce komai dabararka sai kaga wanda ya fika . maganin haka kawai a yi gaskiya.
Comments
Post a Comment