Hikayoyin kaifafa zukata
DAGA LITTAFIN MALAM AMINU KANO
Shugabancin Musulmi
***********************
LBR: Na 002
Ainishin tsantsar shugabanci a tsakanin shugabannin musulmi aka samu.Kuma har yanzu ana samu nan da can .Farkon wadanda za a yi koyi dasu su ne halifofin farko da wasu da suka biyo bayansu.Haka kuma a nan kasar an sami manyan misalai da suka ishe mu koyi. Kuma shugabanci ba wucewa gaba ne kawai ba. Abu mafi wuya ma a cikinsa shine shugaba ya gane cewa sanya shi a gaba din ne biyansa ba ya tara wani abu ba,don tara dukiya ya shugabanci mutane haramun ne.Shugaba kullum yakan tsaya ya tabbatar hakkin mutane na gida da baki,dabbobi da tsirrai. Yazo cikin hadisi cewa sayyadi umar yardar Allah ta tabbata a gare shi kullum ba ya cin abincin dare sai anyi shela a madina ko wanda bai ci abinci ba.An tambaye shi dalili.Ya ce ,don kada Allah ya tambaye shi a ranar hisabi cewa yaya an bashi kiwon mutane amma ya bar daya da yuwwa,shi ko ya kwana a koshe ? Haka kuma yakan ce"wallahi in rakumi ya mutu da kishirwa a kasar islama ni ne da alhaki." An samu cewa halifa umar ibn abdul aziz ya zauna ba wanki har matarsa ta yi magana.Ya ce "wallahi bani da sabulu,kuma bani da kudi " Ta ce,Baka karbowa daga baitulmali?" Ya ce a ranar hisabi zan iya bada dalilin diban kayan amana baHaka kuma an bamu labari cewa shehu usman kullum ya bada tutar mulki zuwa ga wanda ke shugabantar kasa yakan ce,"To modibbo,na tabbata kayi kiwon shanu.In baka yi ba ka tashi ka gani ana yi.Zaka kiyaye cewa bafillace da sanda daya yana iya kora shanu makiyaya komai yawansu. In yaya tsawa shi kadai duk suyi abunda ya ke so.To modibbo,shanu kenan.Amma ka san an baka kiwon mutane .Dukkansu bayin Allah ne yalla musulm ne ko kafiri.Kowane dayansu yana bukatar sanda daban.Ka iya ruke sanduna yawansu ? Baka iyawa .Don haka ka kayaye abu biyar nasu kafin ka nemi biyayyarsu.Sune,rai dukiya jini mutunci addini .Kada ka sayar da kasa domin ta Allah ce ,sai ka basu kyauta.Kuma kada ka bari masu karfi su hana raunana samu.
Rubutu
Adam Muktar
Comments
Post a Comment