Hikayoyin kaifafa zukata

KASHI NA BIYU; YIN ISHARA GA MUTANE.

ZURFIN HIKIMAR HAUSA.

LBR'NA 006

Rubutu; Adam Muktar.

Nan bada dadewa ba a kasar malumfashi an ace marakin wani bafillace.Rahoto ya kai ga yan doka , aka shiga bincike.Wani mai farin kaya mai bincike ya sami labarin kauyen da aka sayar da san amma bai sami sunan wanda aka ce ya saya har ya yanka ya sayar ba. An dai yi masa kwatance. Da ya zo kauyen sai ya zazzagaya a hankali har ya zo wani kofar gida inda ya tarar da wani dan yaro da magariba yana haka a jikin bango.Gidan kuwa a nan aka yanka sataccen marakin.Sai ya tambayi yaron ko a nan ne aka yanka maraki ?. Yaro ya ce ,'I, anan ne. Ashe uban yaron ya saurara. Sai ya ce ,kai waske ," kai da wa ? .Sai yaro ya gane cewa ya yi kuskure da ya amsa don haka ya waske .Sai ya ce, wani mutum ne da abin haushi.Ya same ni ina haka a ramin gafiya ko zan sami naman yau,sa,anan yake tambaya wai a nan aka yanka maraki?. Ni kuma don haushi na ce masa a nan ne .' don haka mai farin kaya sai ya yi gaba.

Comments

Popular posts from this blog

MALIKUSSAIFI LITTAFI NA DAYA 05

MALIKUSSAIFI IBN ZIYYAZANUN LITTAFI NA DAYA-06

MALIKUSSAIFI LITTAFI NA DAYA 04