Hikayoyin kaifafa zukata
DAGA LITTAFIN MALAM AMINU KANO
LBR:NA 005
++++++++++
ALHERI DAYA LADA GOMA
Rubutu; Adam Muktar
Koyaushe mutum ya yi wa wani ko wata alheri ubagiji zai saka masa da kamarsa ribi goma . sai dai in can cikin zuciyarsa akwai wata munakisa. wani dan taliki da matarsa da ya'ya biyu ya wayi gari ba shi da abinda zai ci kuma bashi da ko kwabo . Duk inda ya saba bubbugawa ya je bai samo ko da karfanfani ba. can la,asar sakaliya sai ya dawo gida hannu rabbana. Sai ya ce, da matarsa ta sa ruwa a tukunya ta dafa don ma yara su ga alamar ana abinci. Almuru ta kawo kai ke nan sai ya ji ana sallama a kofar gidanss. Da ya fito sai ga wani ya zo gare shi da cewa ya taimake shi da abinda zai ci domin tun safe bai sa hatsi a baki ba. Sai ya koma cikin gidansa ya ce da matarsa,"Yau ana wata sai ga wata," Kinji abinda mai sallaman nan ya kawo shi ? matarsa ta ce ," To yaya zaka yi ,banda ka sallame shi.? Ya ce," To ai abin da tausayi . Ba wani abu daza mu yi masa .? Ta ce ," Da ba muyiwa kanmu ba.?" Ya ce ," Shi ya san halin da muke ciki ne.? . Shin kazan nan tamu ta fara kwanci ne?" Ta ce," Yau din nan ta fara.; Ya ce ," Je ki dage ta ki debo kwan mu bashi. Matar ta je ta kawo masa kwai ya kaiwa wancan mutum da cewa ba su da komai sai kwan nan .Mutum ya karba ya yi godiya ya tafi .Da gari ya waye sai ga wani bako daga kauye dauke da kwando cike da kwai Ya ce ," Jiya ne bayan al muru sai shaukinka ya zo min rai saboda na dade ban zo ba.Don haka na yiwo sammako na zo don in ganka .Wannan kwai ma da kasuwa na yi niyyar kaiwa .sai na ce gara in kawo ma in jaddada zumunci. Ya shiga da kwai ya kirga sai ya tarar guda dari ne cif cif .Amma guda goma sun fashe. Sai ya tambayi matarsa cewa kwan kaza nan nawa ne ." Ta ce ," Guda goma ne amma daya fashasshe ne . Ya ce ," Wane mutum,Allah da girma yake .Dama ya ce ribi goma yake saka alheri.kinga kwan nan dari ne , kuma goma fasassu ne daidai wa daidai."
Comments
Post a Comment